×

Yadda Za Ku Yi Wa Kasuwancinku TIN Number Certificate Kyauta

Yadda Za Ku Yi Wa Kasuwancinku TIN Number Certificate Kyauta

TIN number itace Tax Identification Number mallakar wannan number abune mai muhimmanci daya daga cikin muhimmancin mallakar shine samun tallafi ko bashi daga gwamnati kokuma wata hukuma ko kungiya.

Mutane da yawa wasu ba susan ya ake samun TIN number ba ba wasu kuma ma basu san me TIN number bah kawai sai insunzo cika wani abu ace ana bukatan wannan TIN number kuma basu dashi

Menene TIN Number?

Ita de tin number ita ce: Tax Identification Number (TIN) wata number ne da ake iya gane mutum da ita koh kamfani kamar dai NIN number kowa da nasa domin biyan kudin Haraji a Nigeria

Menene Amfanin TIN Number?

Wato ita TIN number amfaninta yanada yawa wanda suke kasuwanci koko ince masu company susan hakan sosai

Akwai biyan haraji ita daman wannan number da za a baka anke bance ma ita ne domin biyan haraji akan abubuwa maban banta koko ince akan kasuwancin na kamfaninka

Samun daman cike wani tallafi na gwamnati, sau tari zaka idan kazo cike wani tallafı na kusuwanci koma na daidaiku sai ace kasa TIN number naka a wurin soboda agane shin kana biyan haraji koh baka biya

Bude Account na kamfani ko maka mancinsa, akwai account dinda idan kaje budema shi dai ana bukatan wannan TIN number din kafun ka samu daman bude wannan account din.

YADDA ZA KU YI WA KASUWANCINKU TIN CERTIFICATE

Da farko za ku shiga link ɗin nan na ƙasa https://tinverification.jtb.gov.ng/Home/Index

Da zarar shafin ya bude zai kawo maka jeren abubuwa guda hudu

  • TIN verification portal
  • Access TIN registeretion system
  • Register for TIN non individual
  • Register for TIN (Individual)

Idan taka kai kadai zaka yiwa saika shiga Register for TIN (Individual) idan kuma wata ma’aikata ko kamfani ko wasu kungiya zaka yiwa saika shiga Register for TIN non individual

 

Allah Ya taimaka

Post Comment