Yadda Za Ku Yi Wa Kasuwancinku Smedan Certificate A Kyauta
Zaku shiga shafin su dake wannan adreshin na kasa:https://smedanregister.ng/
Zaku cike sunan kasuwanci ko sana’ar da kuke yi a gurbin cikewa, ku saka nambar waya da kuma adreshin email, sai nambobin sirri (password), da kun saka wannan kun gama da matakin farko.
Mataki na gaba shine bayanin wanne irin kasuwanci ko sana’a kake, shima duka zaka bi ka cike duk bayanan da ake a bukata, sai mataki na gaba wanda zasu karbi bayananka, mataki na karshe zakayi submitting, ka tabbatar duk abinda ka saka daidai ne.
Idan kayi submitting zaka samu sako a email din ka, ko a inbox ko kuma SPAM daga SMEDAN, sai ka bude ka taba inda aka saka SMEDAN CERTIFICATE, zaka samu certificate dinka a file na PDF da zakayi printing ka ajiye, a jikin sa akwai lambar SMEDAN dinka.
Har yanzu shafin yana yi. Ga masu ƙananan kasuwanci da sana’a, wannan dama ce gareku na kuyi rejista da wuri dan more damammaki da dama da zaku habbaka kasuwancin da sana’o’in ku dashi…
A yi share please.
Allah Ya taimaka.
Post Comment